Miliyoyin jama'a na cikin hadari a Bangladesh

Bangladesh
Image caption Bangladesh

Wani sabon bincike ya ce ana saka miliyoyin mutane a Bangaladash cikin hadarin shan sinadarin Arsenic fiye da kima a cikin ruwan sha, abinda kuma ke haddasa mutuwar mutane da yawa.

Binciken wanda aka wallafa a mujallar The Lancet ya nazarci mutane kusan dubu 12 a wata gunduma a cikin wani lokacin da ya kai tsawon shekaru 10.

Binciken ya gano cewar fiye da kashi 20 na mutanen da suka mutu daga cikin wadanda akai nazarin akansu, gurbatar sinadarin Arsenic ne sanadiyar mutuwarsu.

Wakilin BBC ya ce masana ilmin kimiya sun yi kiyasin cewar mutane kusan miliyan 77 ne a Bangladesh suka fuskanci illar sinadarin mai guba tun bullo da rijiyoyin burtsatse a shekarun 1970.