Aikin kula da malalar mai a mashigin Mexico

Shugaban Kamfanin BP Mr. Tony Hayward
Image caption Shugaban Kamfanin BP Mr. Tony Hayward zai mika ragamar aikin malalar mai hannun manajan daraktan kamfanin Bob Dudley

Kamfanin mai na BP ya tabbatar da cewa shugaban kamfanin Tony Hayward zai mika ragamar aikin kula da kwararar mai a mashigin Mexico hannun manajan daraktan kamfanin Bob Dudley.

Shugaban hukumar daraktocin kamfanin ne ya bayyana haka a wata hira da gidan talabijin na Sky Newa kwana guda bayanda Mr. Hayward ya fuskanci kakkausar suka daga wani kwamitin majalisar dokokin Amurka.

Haka kuma kamfanin BP ya musanta zargin da kamfanin Anadarko mai hannun jari a rijiyar man da ke kwarara cewa ganganci da sakacin BP ne su ka haddasa kwararar man tun asali.

Tuni dai kamfanin BP ya ware wani asusu domin tallafawa mutanen da bala'in malalar man ya illata

Malalar man a gabar tekun mexico dai shine wani bala'i mafi muni daya shafi muhalli a kasar Amurka