An sabunta: 19 ga Yuni, 2010 - An wallafa a 16:21 GMT

Ghana 1-1 Australiya

Karawa tsakanin Ghana da Australiya

Karawa tsakanin Ghana da Australiya

An kara tsakanin kasar Ghana da Australiya a cigaba da gasar cin kofin duniya inda akai kunnen doki kowa na da ci daya.

Haka na nufin cewa kasar Ghana ita ce tafi kowacce maki a rukunin D inda take da maki hudu, yayin da Jamus take bi mata da maki uku.

Idan kasar ta Ghana tai nasara a wasan ta na gaba ko kuma tai canjaras to zata kai zagaye na gaba.

Kasar Australiya ce dai ta fara yin nasara a wannan wasa, yayin da Ghana ta farke kwallon a bugun daga kai sai mai tsaron gida.


Sai dai masana kwallon kafa na ganin 'yan wasan Ghana basu yi amfani da damar da suke da ita ba sosai ganin cewa Australiya tana da ragin mutum guda.

Domin ganin sakamakon wasanni kai tsaye da kuma jadawalin rukunai, kana bukatar ka kunna Javascript dinka.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.