Iran ta kashe shugaban musulmi Ahlul Sunna

Shugabankasar Iran Mahmoud Ahmadinejad
Image caption Iran ta ce ta kashe shugaban 'yan tawaye Musulmi Ahlus Sunna da ke kudu maso gabashin kasar.

Iran ta ce ta kashe shugaban 'yan tawaye Musulmi Ahlus Sunna da ke kudu maso gabashin kasar.

Kamfanin dillancin labarai na Iran ya ce an kashe Abdulmalik Rigi ne ta hanyar rataya.

Abdulmalik Rigi ya jagoranci kungiyar Jundullah ne wacce ke tada kayar baya a lardin Sistan-Baluchestan da ke iyaka da kasar Pakistan.

An dora masa alhakin hare-hare da dama da suka haddasa asarar rayuka. An kuma zargeshi da zama karen farautar Burtaniya da Amurka.