Kamaru 1-2 Denmark

'Yan wasan Kamaru
Image caption 'Yan wasan Kamaru

A karawar da aka yi tsakanin Kamaru da kasar Denmark a gasar cin kofin kwallon kafa na duniya, Denmark ta yi nasara akan Kamaru da ci biyu da daya.

Kasar Kamaru ce ta fara samun nasara a wannan wasa lokacin da shahararren dan wasanta Samuel Eto ya dankara kwallo a ragar Denmark.

Amma daga baya Denmark ta farke wannan kwallo, sannan kuma ta sake kara wata.

An taka leda sosai a wannan wasa, inda Kamaru ta sami dama daban daban, amma ta kasa amfani da ita.

Hakan dai na nufin Kamaru ta shiga cikin matsala sosai a wannan gasa ganin ba ta da maki ko daya, sannan wasanta na gaba zata kara ne da kasar Holland wadda ita tafi kowacce kasa maki a wannan rukuni na E.

Tun dai da aka fara wannan gasa kasar Ghana ce kawai ta ci wasa guda tai kunnen doki guda a cikin kasashen Afrika.