Karzai ya kai ziyara birnin Hiroshima

Shugaba Hamid Karzai
Image caption Shugaba Hamid Karzai

Shugaba Hamid Karzai na Afghanistan ya ziyarci Birnin Hiroshima na Japan.

Yaje ne domin ganin yadda birnin ya sake gina kansa bayan da Amurka ta shimfidar da shi da bam din nukiliya kusan shekaru 65 da suka wuce.

Shugaba Karzai, wanda rikicin shekaru 30 ya yiwa kasarsa kaca-kaca, ya zagaya ainihin yankin da aka jefa bam din.

Bam din da aka jefa a Hiroshima a shekarar 1945 ya kashe mutane fiye da 140.