Kotu ta tsare dan tsohon shugaban Nijer Tandja Mamadou

Tsohon shugaban Nijer Tandja Mamadou
Image caption Tsohon shugaban Nijer Tandja Mamadou

A jamhuriyar Nijar kotun birnin yamai ta dau matakin rike dan tsohon shugaban kasar Hadiya -Tulai Tanja da wasu mutane 3 a gidan yari .

Kotun ta zarge su ne da laifin yin amfani da rigar iko ba ta hanyar da ta dace ba,da laifin cin hanci da rashawa,da kuma halitta kudaden haramun, abin da akalin mutanen Barista Sule Umaru ya musunta, yana mai cewa bi-ta-da-kulli ce kawai ta siyasa.

A farkon wannan makon ne dai hukumomin 'yan sanda masu bincike a kan manya-manyan laifufuka suka tsare dan tsohon shugaban kasar da mutanen uku har tsawon kwanaki 3 suna yi musu tambayoyi bisa zargin hannu dumu-dumu a wata harka ta bayar da dillancin lasisin hako ma'adinai ga wani kamfani na kasar Australiya a 2009.