PDP ta raguza masu neman kawo sauyi a jam'iyyar

Shugaban Nijeriya Goodluck Jonathan
Image caption Shugaban Nijeriya Goodluck Jonathan

Jamiyar PDP mai mulki a Nijeriya ta rusa kungiyar nan mai fafutukar kawo sauyi a cikin jamiyar wato PDP Reform Forum.

Jam'iyyar ta ce matakin da kungiyar ta dauka na neman sauyi ya sabawa dokokin jamiyar.

Sai dai kungiyar ta Reform Group ta nuna rashin amincewarta da wannan mataki.

Ta kuma ce nan bada jimawa ba za ta gana da membobinta domin fidda matsayar ta dangane da wanan hukuncin da uwar jamiyyar ta PDP ta dauka akanta.