Dan bindiga dadi ya harbi tsohon babban hafsan Rwanda

Shugaba Paul Kagame na Rwanda
Image caption Shugaba Paul Kagame na Rwanda

Tsohon Babban hafsan hafsoshin sojin kasar Rwanda na cikin halin mutu kwakwai rai kwakwai a Afrika ta Kudu bayan da wani dan bindiga dadi ya harbe shi a ciki.

Janar Kayumba Nyamwasa , mai yin suka ga Shugaba Paul Kagame, na zama ne a Johannesburg tun da ya tsere daga Rwanda cikin watan Fabrairu.

Matar Janar din ta shedawa BBC cewar ba ta da kokwanto cewar wani yunkuri ne na kashe shi.

Janar din ya zargi Shugaba Kagame da cin hanci, zargin da gwamnatin Rwanda ta musanta.

Faransa da Spain sun bayar da sammacen kama Janar Nyamwasa dangane da lamarin da ya haddasa kisan kare dangin 1994.

Patrick Karegeya tsohon shugaban hukumar leken asiri ta soji a Rwanda, sannan kuma wanda shi kansa yake gudun hijira a Afrika ta Kudun, ya ce ko shakka babu Shugaban Rwanda ne ya bayar da umurnin harbin:

Ya ce, bai kamata ma mu yi hasashen ko menene ba. Shugaban Rwanda ya fada lokuta da yawa da kansa. Ya fada kwanan nan cewar zai yi amfani da hama wajen kashe kuda.