An harbi Janar Faustin Kayumba na Rwanda

Janar Faustin Kayumba Nyamwasa
Image caption An harbi Janar Faustin Kayumba Nyamwasa a lokacin da yake dawowa gida daga wata sayayya a Afirka ta Kudu

An harbi wani tsohon babban hafsan sojan kasar Rwanda, Faustin Kayumba Nyamwasa a Afirka ta Kudu.

Tuni kuma aka garzaya dashi zuwa asibiti cikin wani mawuyacin hali.

Matarsa ta bayyana harbin wanda ya auku yayinda suke dawowa gida daga wata sayayya a matsayin wani yunkuri na hallaka maigidannata.

Sai dai a wata sanarwa data aikewa BBC, gwamnatin kasar Rwandan tace tana yiwa iyalan tsohon sojan jaje, tare kuma da yi musu fatan alheri

Janar Kayumba dai na zargin shugabankasar Rwandan da rashawa tare da yin mulki irin na kama karya.

Shi kuwa Shugabankasar Rwandan Paul Kagame ya zargi Janar Kayumba da yukurin yi masa makarkashiya

'Yan sandan kasar Afirka ta Kudu na can na gudanar da bincike