Kaciyar gargajiya na kisa a Afirka ta kudu

Shugaban kasar Afirka ta Kudu Mr. Jacob Zuma
Image caption Yara maza na mutuwa a kasar Afirka ta Kudu sakamakon yi musu kaciyar gargajiya

Jami'an lafiya a Afrika ta kudu sun ce akalla yara maza ashirin da biyu ne suka rasu cikin makonni biyu a lardi guda sanadiyyar kaciyar gargajiya.

Asibitoci a lardin Gabashin Cape sun ce an kwantar da yara da dama bayan da suka kamu da cututtuka sanadiyyar kaciyar kuma ciwon ya yi munin da sai an yankewa wasu daga ciki al'aurarsu.

Mahukunta sun rufe wasu daga cikin cibiyoyin da wanzamai ke yin kaciyar kuma suna shirin tuhumar wanzaman a gaban kotu.

A bara dai yara casa'in da daya ne su ka rasu a lardin na Gabashin Cape bayanda aka yi musu kaciyar.