Binciken masana kimiya kan shayin kofi

Binciken masana kimiyya akan shayin kofi
Image caption Wasu masana kimiyya a Netherlands sun gano cewar shan shayi da kofi akai kai na rage hatsarin kamuwa da ciwon zuciya

Masu binciken kimiyya a kasar Netherlands sun gano cewa shan shayi da kofi ko gahwa a kai akai zai iya rage hatsarin kamuwa da ciwon zuciya.

Masanan sun kwashe shekaru goma sha uku suna nazari kan mutane dubu arba'in kafin su wallafa sakamon binciken nasu a mujallar kungiyar nazarin cututtukan zuciya ta kasar Amurka.

Sakamakon binciken ya bayyana cewa shan shaya kimanin kofi shida a rana guda ko kuma gahwa kofi hudu na rage yiwuwar kamuwa da ciwon zuciya amma abinda ya dara haka kan sa tasirin ya ragu.

Gidauniyar kula da lafiyar zuciya ta Burtaniya ta yi maraba da wannan bincike amma ta yi gargadin cewa shan shayi ba tare da motsa jiki ba, ba wani tasiri da zai yi ga lafiyar bil-adama.