Goodluck Jonathan ya ki tabbatar da ko zai tsaya takara

Shugaba Goodluck Jonathan
Image caption Shugaba Goodluck Jonathan

Shugaba Goodluck Jonathan na Nijeriya ya ki ya ce ko ya Allah zai tsaya takarar zaben Shugaban kasar badi ko kuma a'a.

Mr Jonathan ya shedawa Gidan TV na kasar zai jira har sai lokacin da ya dace domin bayyana shawararsa.

Manema labarai sun ce kokarinsa na yin takarar shugabancin zai iya zama mai cece-kuce.

Shi dai Mr Jonathan ya fito ne daga kudancin kasar inda kiristoci suka fi yawa, sannan kuma wata yarjejeniyar da ba a rubuta ba a jam'iyyar dake mulki ta nuna cewar kamata yayi shugaban kasar na gaba ya fito daga arewa inda musulmi suka fi yawa.