Ministan Jamus ya soki Isra'ila

Firaministan Israila Binyamin Netanyahu
Image caption Firaministan Israila Binyamin Netanyahu

Ministan raya kasa na Jamus, Dirk Niebel ya soki kin da Isra'ila ta yi na barin shi ya shiga Gaza.

Mr Niebel, wanda a halin yanzu yake ziyara a Isra'ila, ya so ganawa da jami'an hukumar kula da yan gudun hijirar Falasdinawa ta Majalisar Dinkin Duniya a Gaza, sannan ya ziyarci wani wurin sarrafa shara da hukumar raya kasashe ta Jamus ke daukar nauyinsa.

Mr Niebel ya ce Isra'ila na yiwa bukatun kanta keta, tare kuma da sawa da wuya kawayenta su fahimci halayyarta.