An kashe shugaban 'yan Sunni a Iran

Shugaban Iran Mahmoud Ahmadinejad
Image caption Shugaban Iran Mahmoud Ahmadinejad

Iran ta ce an kashe Shugaban kungiyar 'yan tawayen 'yan sunni na kudu maso gabacin kasar, Abdulmalek Rigi.

Kamfanin dillancin labarai na Fars mai alaka da gwamnati ya ce an rataye shi a gaban iyalan wasu da fafutikarsa ta shafa a gidan yarin Evin dake Tehran.

Abdulmalik Rigi ya jagoranci kungiyar Jundullah wadda ake dora wa alhakin wani tayar da kayar baya a lardin Sistan-Baluchestan kusa da kan iyaka da Pakistan.

An kuma ce shi ne keda alhakin munanan hare-hare masu yawa, sannan kuma an zarge shi da kasancewa dan leken asiri na Birtaniya da Amurka.

Janar Ali Reza Azimi -Jahed,wani kwamandan rundunar juyin juya hali a Sistan -Baluchestan ya ce mutanen yankin sun yi farin cikin cewar an kashe Abdulmalik Rigi:

Ya ce, a lokacin da abun ya faru mutane sun yi murna.