Matsalar wankan kududdufi tsakanin yara a Borno

Nunkayar yara  a Borno
Image caption Wasu yara na taruwa domin fara nunkaya a wani tafki a garin Maiduguri

A jihar Borno da ke Arewacin Najeriya matsalar wankan kududdufi tsakanin yara na ci gaba da tayar da hankulan mazauna garin Maiduguri, saboda illolin da hakan kan haifar ta fannin lafiya da tarbiyya.

A yayinda Rundunar 'yan sandan jihar ke ci gaba da gargadi ga iyayen yara game da fuskantar barazanar tsaron rayukan su, su kuwa likitoci na bayyana illolin da shiga cikin rafukan ke yi ga lafiyar yaran da ya kamata iyaye su kiyaye.

Ko a makonnin baya ma an rika samun gawarwaki musamman na kananan yara a irin wadannan wurare da galibi aka cire wasu sassan jikin su.

Wakiliyar BBC Bilkisu Babangida ta ziyarci wasu daga cikin rafukan, inda ta ga wasu kananan yara na ta faman ninkaya babu kakkautawa a cikin tafkin dake unguwar Fulatari.

Irin wadannan rafuka da suka yiwa birnin Maidugurin kawanya sun samo asali ne daga babban Tafkin Alau dake kan hanyar Bama.

Kuma kusan duk unguwannin da wadannan tafki ya ratsa kamar su gadar gwange da Lagos Bridge da Maidokiri da gadar kasuwa da sauran wasu unguwanni wurare ne da suka zama matattarar kananan yara maza da mata.

Har ma da almajirai da magidanta wasu na wanka da wanki da kamun kifi da wasannin ninkaya da sauransu.

Mohammadu Kura, wani yaro ne kuma yagayawa BBC cewa yana zuwa ninkaya a kullum a wasu lokutan ma ya kan yi wanki, iyayensa sun sani amma suna jan kunnensa ne kawai yabi a sannu.

"kullum na ke zuwa nan domin nayi wanka da wanki, amma ba na zuwa da daddare," in ji Muhammad

Kiwon lafiya

Dakta Baba Goni Woru na Asibitin Koyarwa na Jami'ar Maiduguri, sananne a fannin cututtuka masu yaduwa.

Ya kuma bayyana wasu daga cikin illolin ma'amalar da yaran keyi da wadannan rafuka kamar su cutar amai da gudawa da fitsarin jini da cuttuka na fata.

" Zai iya kawo yaduwar cututtuka irin su amai da gudawa, da karzuwa da sauran su".

Image caption Yara kan shafe yini guda suna nunkaya

Bulama Malam Ali wani magidanci ne a Unguwar Gwange daya daga cikin unguwannin dake da irin wadannan rafuka.Kuma ya shaidawa BBC cewa:

"Yawancin wadannan yara suna zuwa ne ba tare da sanin iyayen su ba, ya kamata iyaye su dinga tsawatarwa 'ya'yan su".

"Iyaye nada rawar takawa"

Illolin wanka ko kuma wasanni a wadannan rafuka da yaran kanyi ba wai ya tsaya ne kawai kan kamuwa da cututtuka ba.

Sukan fada hannun bata gari musamman ma ga yaran da kan yi mu'amala da rafukan da dare da wasu lokuta akan tsinci gawarwakin yara da aka cire wasu sassan jikin su.

Sai dai kwamishinan 'yan sandan jihar Borno Ibrahim Abdu inda yace iyayen yara su ke da hakkin lura da yaran su duk da cewar suma jami'an tsaro suna bakin kokarin su wajen kare rayukan jama'a ganin irin abubuwan da suka faru a baya.

"Malamai da iyaye da masu unguwanni suna rawar takawa wajen tabbatar da tarbiyyar yara, wanda hakan zai taimaka wajen kiyaye lafiyar su".

Bukatar da keda a akwai dai itace ta iyayen yara da malaman tsanagaya su kula da yadda yara ko kuma almajiran su ke kai komo a cikin irin wadannan rafuka.