Kamfanin BP yayi sakaci inji ma'aikaci

Malalar rijiyar man kamfanin BP a mashigin tekun mexico
Image caption Wani jami'in kamfanin BP yace ya gano murfin rijiyar man na yoyo makonni kadan kafin aukuwar balain malalar man

Wani ma'aikaci a rijiyar da ke kwararar da mai a mashigin tekun Mexico ya shaidawa BBC cewa ya gano murfin rijiyar na yoyo makonni kadan kafin afkuwar fashewar da ta jawo malalar man.

Aikin murfin dai shi ne ya toshe rijiyar duk lokacin da aka samu wani hadari.

Tyrone Benton ya ce an sanar da kamfanin BP a kan kari da kuma kamfin Transocean wanda shi ne ya mallaki na'urar hakar man.

Sai dai a cewar Mr. Benton kamfanin BP ya ki gyara murfin saboda hakan zai jawo dakatar da aiki wanda zai haddasa asarar dala rabin miliyan a kowace rana.

A nasa bangaren kamfanin BP ya ce hakkin Transocean ne ya kula da na'urorin da ake aiki da su a rijiyar.