Kotu ta daure Bello Lafiagi da wani na hannun damarsa

 Alamar kotu
Image caption Alamar kotu

Wata babbar kotu da ke a Lagos ta daure tsohon shugaban hukumar NDLEA mai yaki da fatucin miyagun kwayoyi, Alhaji Bello Lafiya tsawon shekara hudu a gidan yari.

Hukumar ICPC mai yaki cin hanci da karbar rashawa ce ta shigar da karar.

Ta zargi tsohon shugaban hukumar ta NDLEA da wani na hannun damarsa, da karbar kudade kusan Euro dubu dari da sittin da biyar, daga hannun wani da aka zarga da fataucin hodar Ibilis ne.

Mutanen biyu da aka samu da laifuka 7 sun ce za su dauakaka kara.