Za'ayi zaben raba gardama a kasar Poland

Zaben Shugabankasa a Poland
Image caption Za'a gudanar da zaben raba gardama na shugabankasa a kasar Poland makonni biyu masu zuwa

Sakamakon farko na zaben shugaban kasar Poland na nuna cewa shugaban rikon kwarya Broniswav Komorowski na jam'iyyar 'yan jari hujja ta Civic Platform ne ya samu rinjayen da bai kai rabin adadin kuri'un da aka kada ba.

Sakamakon haka, za'a yi zaben raba gardama nan da makonni biyu tsakaninsa da abokin takarar da ke dafa masa baya, Yaroswav Kachinski, dan uwan tagwaitakar marigayi shugaban kasa Lek Kachinski.

Mr. Komorowski ya shaidawa magoya bayansa cewa yana hangen nasara a zaben raba gardamar da za'ayi a makonni biyun masu zuwa.