Bankuna sun rufe a Okigwe na jihar Imo

takardun kudin Nijeriya
Image caption matsalar fashi a wasu bankuna ta hana su budewa a Okigwe

A Najeriya, ma'aikatan bankuna suna ci gaba da gudanar da wani yajin aiki na tsawon mako guda a garin Okigwe, wato daya daga cikin garuruwa mafi girma a jihar Imo.

Ma'aikatan sun bi wannan mataki ne a sakamkon matsalar 'yan fashi da makami da ke yawan addabar bankuna a garin.

Hakan dai na faruwa ne duk da tabbacin kara matsa kaimi da hukumomin 'yan sanda ke cewa suna yi wajen kyautata sha'anin tsaro a shiyyar kudu maso gabashin Najeriyar.

Ko a kwanakin baya, bankuna a garin Aba, da Onitsha sun dauki irin wannan mataki, lamarin da ya kai ga kara tura ma su jami'an tsaro.