Burtaniya za ta tsuke bakin aljihunta

Sakataren kudin Burtaniya
Image caption Sakataren kudin Burtaniya George Osborne dauke da jakar kasafin kudin kasar na bana

Sabuwar gwamnatin hadin gambizar Birtaniya, ta gabatar da kasafin kudinta, inda ta dauki tsauraran matakan tsuke bakin aljihunta, da zummar cike babban gibin da ke akwai.

Sabbin matakan da gwamnatin ta dauka sun hada da karin kashi 2 da rabi na harajin VAT ko TVA da rage yawan kudaden da gwamnatin ke kashewa wajen taimakawa jama'a da dakatar da yin karin albashi ga ma'aikatan gwamnati da kuma haraji a kan bankuna.

Babbar jam'iyya adawa ta Labour ta yi gargadin cewa tsuke bakin aljihun gwamnati haka cikin gaggawa, yana iya jefa Burtaniya cikin wani hali na tabarbarewar tattalin arzikinta.

Sakataren kudin kasar, George Osborne, dan jam'iyyar Conservative ta masu ra'ayin 'yan mazan jiya, ya shaida wa majalisar dokokin kasar cewa, rage kudaden da gwamnati ke kashewa, da kuma kara kudaden haraji, suna da mahimmanci matuka wajen cike gibin.

Sai dai a ganin babbar jam'iyyar adawan Labour, sabon kasafin kudin, zai yi illa ga bunkasar tattarlin arzikin kasar.

Abinda wannan kasafin kudin ya kunsa, sun hada da wadansu tsauraran matakai da kasar bata taba fuskantar irinsu ba.

Adadin gibin da Burtaniya ke fama da shi ya kai dala biliyon 230 .

Ministan Kudi George Osborne dai ya bayyanawa 'yan majalisar cewa ragin da za'a yi a kudaden da ake kashewa da kuma karin haraji nada matukar mahimmanci wajen rage gibin kasafin kudin Birtaniya.

Mista Osborne ya fara ne da bayyana mahimmancin kasafin kudin wanda yace na gaggawa ne.

Yace ana bukatar wannan kasafin kudin ne domin shawo kan bashin da kasar ke fama da shi.

"Ana bukatar wannan kasafin kudin domin baiwa tattalin arzikin kasar tabbaci".

"Babu yanda za'a yi a iya gujewa yin haka. Kuma ba zan boyewa al'ummar Burtaniya wannan mawuyacin matakin ba, ko kuma na yi kokarin lullubesu a cikin kundin kasafin kudin ba," in ji Osborne

Mista Osborne dai ya sake jaddada cewa babu wani zabi na hakika da za'a yi wajen ceto tattalin arzikin da ya wuce yin wannan ragin:

Yace yanzu kam wadansu na bada shawarar cewa akwai zabi a tsakanin magance bashin da ake bin mu da kuma ci gaban tattalin arziki.

Wannan kam sam ba zabi ne mai kyau ba. Matsalar da ake fama da ita a kasashen dake amfani da kudin Euro na nuni ne da cewa idan har bamu magance matsalar bashin mu ba, ba za'a samu cigaban tattalin arziki ba.

Ra'ayin masana

To sai dai wadansu masana na ganin cewa wannan matakin na iya sake tsunduma Burtaniya cikin yanayin durkushewar tattalin arziki.

Will Hutton wani mai sharhi ne wanda ya bayyanawa BBC cewa wannan matakin kamar wata babbar caca ce:

"Yace wannan babban aikin gwaji ne da muka saka kan mu a ciki. Bana jin wata kasa za ta iya da wannan tsuke bakin aljihun, balle kuma iya daukar nauyin kanta ta fuskar tattalin arziki".

Wannan dai shi ne babban ragin da wata mambar kasa a cikin kungiyar bunkasar tattalin arziki da cigaba wato OECD ta taba yi a wannan zamanin.

"Wannan dai abu ne da babu tabbas. Ta yiwu yayi aiki, amma dai kam wannan gwaji ne," a cewar Hutton

Sauran kasashen Turai

A duka fadin nahiyar turai dai kasashe na daukar wannan matakin rage gibin da suka samu a kasafin kudaden su domin gujewa afkawa cikin irin matsalar da kasar Girka ta samu kan ta a ciki.

Jamus ce dai ta fara bude hanya inda ta bayyana yin ragin da bata taba yi ba tun bayan yakin duniya na biyu.

Kasar Spaniya ma dai ta aiwatar da nata sauyen wadanda suka fuskanci suka daga kungiyoyin kwadago na kasar.

Shugaba Obama na Amurka ya goyi bayan matakan da kasashen Turan ke dauka, domin a cewar sa akwai bukatar kaucewa sake komawa gidan jiya a rikicin tattalin arzikin da duniya ta yi fama da shi.