Rashin tabbas a makomar Janar McCrystal

Janar Stanley McChrystal.
Image caption Kwamandan dakarun Amurka a Afghanistan. Mukaminsa, tana kasa tana dabo.

Fadar White House ta ki ta ce ko babban kwamandan sojan Amurka dake Afghanistan, Janar Stanley McChrystal, zai ci gaba da aikinsa ko kuma a'a, bayan shi da mukarrabansa sun yi wasu kalamai na ba'a ga wasu manyan jami'an gwamnatin Amurkan.

Wani kakakin fadar ta White House, Robert Gibbs ya ce tuni aka nemi Janar din da ya koma gida.

Daga cikin wadanda aka yi wa ba'ar, akwai Jim Jones mai ba shugaba Obama shawara kan harkokin tsaro, wanda aka kwatanta da chali-chali.

Mr Gibbs dai ya ce komai na iya faruwa game da mukamin na Janar McChrystal.