Najeriya na son shaida shari'ar Abdulmutallab

Umar Abdulmutallab
Image caption Gwamnatin Najeriya ta ce tana so ta tabbatar da an bi doka wajen yiwa Umar Abdulmutallab shari'a

Gwamnatin Najeriya ta bukaci wata kotun Amurka ta ba ta damar kasancewa a wurin da za a yi shari'ar dan Najeriyar nan da ake zargi da kokarin tarwatsa wani jirgin saman fasinja na Amurka a samaniyar Detroit ranar jajiberan Krismetin da ya gabata.

Gwamnatin Najeriya dai ta ce tana so jami'anta su kasance a wurin shari'ar ne saboda ta tabbatar da cewa an bi doka da tsari wajen yiwa Umar Faruk AbdulMutallab shari'a.

Gwamnatin Najeriyar ta kuma bukaci a ba ta dukkan takardun da ke gaban alkali dangane da wannan shari'a.

Lauyoyin Najeriyar sun ce kasar ba ta bayar da fuska ga ayyukan ta’addanci to amma, a cewarsu, wannan shari’a ce mai daukar hanakalin jama’a wadda kuma ta ke cike da sarkakiya.

A watan Janairu ne dai aka tuhumi Abdulmutallab da aikata lafuffuka shida, ciki har da yunkurin amfani da makamin da zai iya hallaka mutane da dama.

Mafi tsananin hukuncin da za a yanke mishi dai shi ne daurin rai-da-rai idan aka same shi da laifi, kamar yadda Antoni Janar na Amurka, Eric Holder, ya sanar lokacin da yake bayyana tuhumar.