Daukar dawainiyar basusukan bankuna a Najeriya

Majalisun dokoki a Najeriya sun amince da kafa wani kamfani da zai dauki dawainiyar kula da basussukan bankuna wadanda aka kasa biya.

Wannan kamfani, mallakar babban bankin Najeriyar, CBN, zai sayi basussakan da suka yi tauri ne daga hannun bankunan kasar, domin tabbatar da cewar irin wadannan basussuka ba su janyo durkushewar bankunan ba.

Babban bankin Najeriyar, wanda ya dade yana godon ganin an kafa wannan kamfani, ya ce yin hakan zai taimaka wajen tabbatar da cewa, talakawa ba su yi asarar irin kudaden da suke kai wa ajiya a bankunan kasar ba.