'Yan adawan Ivory Coast sun zargi Shugaba Gbagbo

Shugaba Laurent Gbagbo
Image caption Sau bakwai ana jinkirta yin zabe tun bayan karewar wa’adin mulkin Shugaba Gbagbo shekaru biyar da suka wuce

Manyan jam'iyyun adawa na kasar Ivory Coast sun zargi shugaban kasar, Laurent Gbagbo, da laifin kokarin yin zagon kasa ga gyaran harkar zabe a kasar ta hanyar bayar da umarnin a binciki Ministan Harkokin Cikin Gida Désiré Tagro bisa zargin aikata cin hanci da rashawa.

Manufar binciken ita ce gano ko Mista Tagro da wadansu mutanen, watakila har da Firayim Minista Guillaume Soro, sun karbi cin hancin euro miliyan goma sha biyar daga wani kamfanin kasar Faransa mai kera injinan kada kuri’a.

Wani jigo a bagaren 'yan adawar, Alphonse Djédjé Mady, ya ce shugaban kasar ta Ivory Coast yana kokari ne kawai ya kawo cikas ga aikin yin rajistar masu zabe da nufin sake jinkirta yin zaben kasa baki daya.

Sau bakwai ana jinkirta yin zabe a kasar tun bayan karewar wa’adin mulkin Shugaba Gbagbo shekaru biyar da suka wuce.

‘Yan adawa dai na kira da a kammala rajistar masu kada kuri’a kafin karshen watan Yuli saboda a samu damar yin zabe a watan Agusta.