Na yi takaicin rashin musuluntar Michael Jackson- Jermaine

Jermaine Jackson a lokacin janazar Michael Jackson
Image caption Jermaine Jackson ya taka rawa sosai a lokacin janazar Michael Jackson

Yayinda ake ci gaba da bukukuwan cika shekara guda da mutuwar shahararren mawakin nan Michael Jackson, yayan mawakin Jermaine Jackson, ya ce ya yi takaicin rashin karbar addinin musulunci da kanin nasa bai yi ba.

A wata hira ta musamman da yayi da BBC, Jermaine Jackson, ya ce da Michael Jackson ya shiga musulunci, da bai samu kansa a wancan hali ba, abinda har ya yi sanadiyyar rasuwar sa.

"Yace kodayaushe nakan yi takaicin cewa ban samu damar ceto rayuwar sa ba".

Ga dai yadda hirar tasa da BBC ta kasance:

BBC: To ko menene dalilinka?

Jermaine: Idan da Michael Jackson ya shiga musulunci, da tuni yana raye. Saboda idan kana da yakini a kan abinda kake aikatawa da kuma wadanda suke kewaye da kai, to lallai rayuwarka za ta inganta, domin Allah zai taimake ka.

Ya kara da cewa yana karanta litattafai da dama, na sayo masa wasu daga Saudi Arabiya da kuma Bahrain. Ni ne na fara kai shi Bahrain saboda ina so ya bar Amurka domin rayuwar Amurka na jefa shi cikin mawuyacin hali.

BBC: Sai dai bai so ya shiga musuluncin ba ko kuwa?

Jermaine: Ba wai ba ya so ya shiga musulunci bane. Duka masu gadinsa musulmai ne saboda ya amince da musulunci, kuma ganin wadannan mutane tare da shi zai taimaka Allah ya bashi kariya ko don saboda su.

Image caption Jermaine Jackson da Michael Jackson lokacin suna yara

BBC: Shin ko ka yarda da zargin da aka yi masa na cin zarafin yara?

Jermaine: Ai kotu ta wanke shi game duk wadannan zarge-zargen. Yaron da ake magana a kansa Jordan Chandler ya ce bai taba taba shi ba. Abinda ya sa kuma mahaifinsa ya kashe kansa.

Kuma da wannan ne kafafen yada labarai suka yi ta zuzuta lamarin suna sukar dan uwana a kan abinda bai aikata ba, kuma har yanzu wasu ba su amince da hakan ba.

Ya ce kaunar da aka nunawa dan uwana lokacin da ya rasu, ita ya kamata a nuna masa lokacin da yake raye. Hukumar bincike ta FBI a Amurka ta bincike shi har na tsawon shekaru 17, amma ba ta same shi da wani laifi ba.

Sai daga baya suka zo suna yabonsa, a gani na irin wannan yabon ya kamata su nuna masa tun yana raye, kuma da hakan ya karfafa masa zuciya.

BBC: To ko yaya rayuwa take bayan mutuwar Michael Jackson?

Jermaine: Hakika da wahala, ba zan iya bayyanawa da fatar baka ba. Abu ne wanda sai ka dandana sannan za ka san yadda yake. Amma mun fara sabawa, sai dai ba zamu iya mantawa ba domin akwai tsauri sosai.

BBC: Ko rashinsa na yin tasiri ga rayuwarka?

Jermaine: Hakika ina mutukar kewar rashinsa, saboda mun dade muna tare tun muna yara, don haka har yanzu ina tuna rayuwar mu wacce ta hada da tafiya makaranta da kade-kade wadanda muka dade muna yi tare.

Na dade ina taimaka masa wajen harkokin waka. Kuma ya kafa tarihi sosai a wannan fage domin kullum fatansa shi ne na ganin an samar da duniya wacce ke cike da adalci da kuma daidaito, kuma da haka yayi fice.

BBC: Ka yi bayanai ga manema labarai lokacin da ya rasu a birnin Los Angeles. Abinda yasa ake ganin kamar ka karbe ragamar gidan naku?

Jermaine: Ba na kallon abin ta wannan fuska. Na yi abinda ya dace, kuma ba na son sauraren maganganun da ba su da tushe game da gidanmu, abin yana damuna matuka. Kuma idan kafafen yada labarai suka kauce, to dole ne na dawo da su kan turba.

kaunar da aka nunawa dan uwana lokacin da ya rasu, ita ya kamata a nuna masa lokacin da yana raye. Hukumar bincike ta FBI a Amurka ta bincike shi har na tsawon shekaru 17, amma ba ta same shi da wani laifi ba. In ji Jermaine Jackson

BBC: A lokacin da Michael ya rasu, kace ka fahimci irin halin da suka sanya shi a ciki. Su wanene kake nufi?

Jermaine: Ina nufin 'yan jarida da masu shirya finafinan Hollywood na Amurka, ina la'akari da irin bita-da-kullin da aka dinga yiwa dan uwana lokacin da yana raye, amma kuma bayan mutuwarsa sai aka dinga nuna masa soyayya. Wacce ya kamata ace an nuna masa tun lokacin yana da rai.

BBC: Ko ya zai tunkari aikin kare tarihin da Michael ya kafa da kuma gidan baki daya?

Jermaine: Wannan ba aiki na bane ni kadai, abu ne da ya ta'allaka a kan kowanne mamba na gidan. Domin dukanmu 'yan uwa ne tun kafin a fara maganar waka da kuma batun shahara a rayuwa. Don haka za mu ci gaba da kasancewa a matsayinmu na 'yan uwa.

Dangane da iyalinsa, Jermaine Jackson ya ce a yanzu ina da 'ya'ya shida maza biyar da mace daya, kuma idan na samu mata biyu nan gaba, to zan zamo kamar baba na, domin yana da 'ya'ya tara, shida maza uku mata.

BBC: Shin ko ka tsara sunayen da za ka samu su?

Jermaine: Ina shirin sa musu suna Mecca da Medina.