An yi gangamin neman zabe na gari

Taswirar Najeriya

A birnin Ikko dake kudancin Najeriya, wasu 'yan siyasa daga bangaren adawa da kuma wasu masu fafutukar kare hakkin jama'a sun shirya wani gangami, domin neman a gudanar da zabe nagari, kuma ingantacce a Nijeriya.

Daya daga cikin bukatun masu gangamin shi ne na ganin an sake kundin rajistar masu zabe, domin a cewarsu ba su yarda da ingancin wanda ake da shi yanzu ba.

Gangamin dai kungiyar "save Najeriya" ce ta shirya shi, kungiyar data shige gaba wajen ganin an mika ragamar shugabancin Najeriya ga shugaba Goodluck Jonathan.

Harkar zabe a Najeriya batu ne dake dada jan hankalin a ciki da kuma a wajen kasar.