Obama zai dauki mataki kan Janar McChrystal

Shugaba Onama da Janar McChrystal
Image caption Shugaba Obama ya ce sai ya gana da Janar McChrystal zai yanke shawara a kan matakin da zai dauka

Shugaban Amurka Barack Obama ya ce zai so ya yi magana kai tsaye da Janar Stanley McCrystal kafin ya yanke shawara a kan matakin da zai dauka a kan kwamandan na dakarun Amurka a Afghanistan.

Shugaba Obama dai ya zabo Janar McChrystal ne don ya jagoranci sojojin Amurka a Afghanistan saboda shi ne mutumin da ake ganin yana da hangen nesan da zai kai ga yin nasara.

Sai dai a yanzu shugaban na Amurka zai yanke shawara ne a kan ko zai sallami hafsan sojan saboda rashin aiki da hangen nesan a yayin da ya ke mu'amala da wani dan jarida.

Janar McCrystal din da wadanda ke aiki tare da shi sun yi wata katobara ce a wata mujallar Amurkan inda suka yi izgili ga manyan jami'an gwamnatin Obama.

An bayar da rahoton cewa ran shugaban na amurka ya baci ko da yake, kamar yadda ya saba, bai nuna bacin ran nasa a bainar jama'a ba.

“Janar McChrystal na kan hanyarsa ta dawowa.

“Zan gana da shi kuma Sakataren Tsaro Robert Gates ma zai gana da shi.

“Ina ganin akwai alamun rashin hangen nesa a abin da ya fada a mujalla shi da wadanda ke tare da shi.

“To amma sai na gana da shi kai tsaye kafin in yanke shawara a kan matakain da zan dauka”, inji Shugaba Obama.

Wannan dai mawuyacin al'amari ne a siyasance.

Korar Janar McChrystal za ta nuna cewa Shugaba Obama ba ya tsoron tauna tsakuwa a duk lokacin da wani jami'in gwamnati ya yi ba daidai ba, komai girmansa.

Sai dai kuma hakan na nufin kawar da wani jarumin hafsan soja wanda ya yi amanna cewa Amurka za ta yi nasara a yakin da ta ke yi a Afghanistan.