'Yanzu aka fara rigima' -'Yan majalisa

Kakakin Majalisar Wakilai ta Najeriya, Dimeji Bankole
Image caption 'Yan Majalisar da aka dakatar sun ce babu ja da baya a kokarinsu na tsige Kakakin Majalisar Wakilai Dimeji Bankole

A Najeriya, 'yan Majalisar Wakilan da aka dakatar daga majalisar sun ce ba za su ja da baya ba a kokarin da suke yi na neman a binciki zargin aikata ba daidai ba da suke yiwa kakakin majalisar, Dimeji Bankole.

Wannan lamari dai ya haddasa doke-doke da hargitsin da ya ma kai ga raunata wani dan majalisar a jiya.

'Yan majalisar da ke kiran kansu 'The Progressives' su goma sha daya dai sun shafe makwanni suna shan alwashin tsige kakakin majalisar, Dimeji Bankole.

Daya daga ‘yan kungiyar, Hon. Abba Anas Adamu, ya ce matakin dakatar da su da aka dauka bai ba su mamaki ba, kuma za su dauki mataki.

“Muna so mu tabbatar masu cewa yanzu aka fara wannan rigimar; kuma insha-Allahu gaskiya tana bangarenmu”, inji Hon. Anas.

Ya kuma ce tuni sun fara ganawa da lauyoyinsu don kai batun gaban kotu

Tuni dai masu lura da al'amura a Najeriyar suka fara tofa albarkacin bakinsu dangane da doke-doken da aka yi a zauren Majalisar Wakilan.

Awwal Musa Rafsanjani na kungiyar CISLAC mai sa ido a kan harkokin da suka shafi majalisun dokokin kasar ya bayyana cewa abin da ya faru a zauren Majalisar Wakilan wani babban abin takaici ne ga dimokuradiyyar Najeriya.