Nijar ta dage haramcin da aka dorawar MSF

Yaro mai fama da cutar tamowa

Gwamnatin mulkin soja a Jamhuriyar Nijar ta ba kungiyar agajin likitocin nan ta kasar Faransa, Medecins Sans Frontieres izinin dawowa domin ci gaba da ayyukan kula da daukar dawainiyar yara kanana masu fama da tamowa a jahar Maradi.

Ofishin ministan cikin gida da ofishin ministan kiwon lafiya ne suka tabbatar da haka.

Kakakin kungiyar ta Medecins Sans Frontieres Mista Guillaume(Giyom) ya ce sun fara yin shawarwari da ofishin ministan kiwon lafiya dangane da soma ayyukan nasu a Nijar.

A shekara ta 2008 ne gwamnatin shugaba Tandja Mammadu ta kori kungiyar ta Medecins Sans Frontieres daga Nijar bisa zargin keta dokokin kasa.