Afghanistan ba ta so a sauke McChrystal

Janar Stanley McChrystal
Image caption Janar McCrystal zai gana da Obama a Washington

Gwamnatin Afghanistan ta ce idan aka sauke babban hafsan sojin Amurka, janar McChrystal daga jagorantar dakarun NATO a kasar, hakan ba zai taimaka wajen samar da zaman lafiya a Afghanistan ba.

Janar Stanley McChrystal zai gana da shugaba Obama idan an jima a birnin Washington, inda zai yi bayani kan wasu kalamai na batanci da ya yi a kan wasu jami'an gwamnatin Amurkar cikin wata mujalla.

Daya daga cikin abubuwan da aka fahimta dai shi ne cewa Janar McChrystal ya rubuta takardar murabus, hukuncin amincewa da takardar ko kuma a kyale shi ya cigaba da aikinsa na ga Mr. Obama

Shugaba Obama ya fusata da kalaman na Janar McChrystal, kamar yadda kakakinsa ya bayyana.