Dan majalisar wakilan Najeriya Ustine Nwachukwu ya gurfana gaban kotu

Rundunar 'yan sandan Najeriya a Abuja ta gurfanar da wani dan majalisar wakilan kasar, Ustine Nwachukwu a gaban wata kotun Majistare, tana tuhumarsa da amfani da makami a zauren majalisar, wajen raunata daya daga cikin takwarorin aikinsa.

A jiya ne dai wata hatsaniya ta kaure a zauren majalisar wakilan, bayan kokarin da wasu 'yan majalisar na kungiyar The Progressives suka yi, na neman majalisar ta binciki zargin yin rub-da-ciki akan dukiyar jama'a da suke yi wa kakakinta, Dimeji Bankole.

A lokacin hatsaniyar wasu 'yan majalisa sun jikkata, kuma an yayyaga wa wasun tufafinsu.