Shugaba Obama ya kori Janar McChrystal daga shugabancin rundunar kawance a Afghanistan.

Janar Stanley McChrystal
Image caption Janar Stanley McChrystal

An sauke ba-Amurken nan, babban kwamandan dakarun kawancen kasashe a Afghanistan, Janar Stanley McChrystal, daga kan mukaminsa

Shugaba Obama ya amince da abin da ya kira murabus din nasa, ba domin yana so ba, amma ya ce maganganun batancin da wasu mukarraban Janar din suka yi kan gwamnatinsa cikin wata mujalla, ba su dace ba.

Bayan da aka bukaci Janar McChrystal ya je Washington, an maye gurbinsa da Janar David Patraeus, tsohon kwamandan dakarun Amurkar a Iraki.

Gwamnatin Afghanistan, wadda ta ce sauke Janar Stanley McChrystal zai shafi yanayin tsaro a kasar, ta ce zata mutunta shawarar da Amurkar ta zartar.