An tsige mataimakin gwamnan Bayelsa

Nijeriya
Image caption Nijeriya

A Nijeriya an tsige mataimakin gwamnan Jihar Bayelsa dake Kudu maso kudancin Nijeriya, Chief Peremobowei Ebebi.

'Yan Majalisar dokokin jihar su goma sha takwas, daga cikin ashirin da hudu, suka kada kuri'ar goyon bayan tsige mataimakin gwamnan.

Da ma dai an dade ana kai ruwa rana tsakanin gwamnan jihar Mr Timiprye Sylva, da mataimaikin nasa, kuma wannan mataki da 'yan majalisar dokokin suka dauka ya biyo bayan sakamakon wani bincike da wani kwamitin gwamnatin jihar ya gudanar ne, inda suka zargin mataimakin gwamnan da rashin iya aiki.