An yi bukin ranar yaki da miyagun kwayoyi a Kamaru

Hodar iblis ta cocaine
Image caption Hodar iblis ta cocaine

Matsalar amfani da miyagun kwayoyi matsala ce da ke kara kamari tsakankanin matasa a Kamaru.

Rahotanni na nuna cewar akwai matasa da shekarunsu suka kama daga 15 zuwa 20 dake mu'amala da miyagun kwayoyi wurin sha ko kuma sayarwa.

An bayyana haka ne a wajen kaddamar da bikin ranar yaki da miyagun kwayoyi a karo na 23 da Ministan kiwon lafiya Andre Mama Fouda ya jagoranta.

Ministan ya sake fadakar da matasa da su guji, wannan dabi'a , su kuma fahimci irin illar da take yi ga al'umma.