Shugaba Obama ya gana da takwaran aikinsa na Rasha

Shugaba Obama da Shugaba Medvedev
Image caption Shugaba Obama da Shugaba Medvedev

Shugaba Obama da takwaransa na Rasha, Dmitry Medvedev sun tattauna kan batutuwa da dama a Washington, a ziyarar Mr. Medvedev din na farko a Amurka.

Shugaba Obama dai ya bayyana Mr. Medvedev a matsayin aboki na kwarai, abin dogaro kuma tattaunawarsu tayi nasara.

Wakiliyar BBC tace, a bara an sake kyautata dangantaka siyasa tsakanin Amurka da Rasha, amma yanzu hankalinsu ya karkata ne kan dangantaka ta fuskar tattalin arziki.

Mr. Medvedev yace Rasha da Amurka sun dau matakan kyautata dangantaka tsakaninsu da zai kai ga samar da zaman lafiya a duniya.

Ya kara da cewa ziyararsa na da niyyar bada wata babbar damar.