PDP ta yi suka kan 'yan Majalisar Wakilan Najeriya

Kakakin Majalisar Wakilai ta Najeriya, Dimeji Bankole
Image caption Jam'iyyar PDP ta umurci jagororin Majalisar Wakilai su yi mata bayani a kan hatsaniyar da ta kaure a majalisar

Jam'iyyar PDP mai mulki a Najeriya ta yi Allah wadai da abin da ta kira abin fallasar da ya faru a Majalisar Wakilai ta kasar.

A wata sanarwa da ya fitar, kwamitin gudanarwa na jam'iyyar ta PDP ya bayyana takaicin jam'iyyar dangane da abubuwan da suka wakana a zauren Majalisar Wakilan, inda wadansu 'yan majalisar, wadanda yawancinsu 'ya'yan jam'iyyar ne, suka ba hammata iska a bainar jama'a, ciki har da yara 'yan makaranta da suka je don ganin yadda majalisar ke aiki.

Kwamitin gudanarwar ya ce ya yi takaicin yadda 'yan majalisar suka yi watsi da wasiyyar da ya yi musu tun farko cewa su kai zuciya nesa su kuma sasanta bambance-bambancen da ke tsakaninsu ta hanyar musayar ra'ayi.

Sai dai sanarwar ta jam'iyyar PDP, wadda ta yi amfani da kakkausan lafazi, ba ta yi bayanin ko za ta dauki matakin ladabtarwa a kan wadanda al’amarin ya shafa ba.

To amma kwamitin gudanarwar jam'iyyar ya ce tuni ya gayyaci shugabannin majalisar don ganawa da su, ya kuma bukaci dukkan 'ya'yan jami'yyar da suka yi uwa suka yi makarbiya a al'amarin su yi masa bayanin irin rawar da ko wannensu ya taka, don jam'iyyar ta san irin matakin da za ta dauka.

Jam'iyyar ta ce abin da ya farun ya saba da manufofin shugaban kasar, da ma na sabon shugaban jam'iyyar, na karfafa kamun kai da mutunta juna a tsakanin al'umma, don haka ta nemi 'yan majalisar su nemi gafara a wajen 'yan Najeriya.

Tuni dai wadansu masana harkokin siyasa a Najeriyar suka fara zargin cewa irin wannan yanayi na ba hammata iska a Majalisar Wakilan alama ce ta rashin dattaku.

Sai dai 'yan majalisar sun ce samun sabani tsakanin 'yan majalisa ba wani sabon abu ba ne.

Ranar Talatar da ta gabata ne dai zauren Majalisar Wakilan ya koma fagen dambe bayan wadansu 'yan majalisa sun yi yunkurin gabatar da bukatar a tsige kakakin majalisar, Dimeji Bankole, bisa zargin aikata cin hanci da rashawa.