Timothy Geithner ya kalubalanci kasashen Turai

Timothy Geithner
Image caption Timothy Geithner

Sakataren Baitulmalin Amurka, Timothy Geithner ya bukaci gwamnatocin kasashen Turai da su mayar da hankali a kan samun yalwa domin taimakawa farfadowar tattalin arzikin duniya.

Mr Geithner na magana ne yayinda shugabanin kasashen duniya ke shirin taron kolin kungiyar kasashe takwas da suka fi arzikin masana'antu ta G8, da kuma ta kasashe 20 masu karfin arzikin na duniya a Canada.

Ya ce duniya ba za ta iya dogara a kan Amurka, kasar da ta fi kowace karfin arziki a duniya, kamar yadda ya faru a baya ba.

Kiran na Mr Geithner dai ya jaddada irin bambance-bambamcen da ake da shi wajen tunkarar lamarin tsakanin Amurka da Kungiyar Tarayyar Turai.

A cikin makunnin da suka wuce dai abinda ake jaddadawa a Turai shi ne zabtare gibin kasafin kudi.