Kotu ta dawowa da Garba Gadi mukaminsa

Taswirar Nijeriya
Image caption Taswirar Nijeriya

A Nijeria, wata kotu a jihar Bauchi ta yanke hukuncin mayar da tsohon mataimakin gwamnan jihar Alhaji Garba Gadi da aka tsige daga kan mukaminsa.

Kotun karkashin jagorancin mai shariah Haruna Tsammani, ta bayar da umarnin cewar a mayar da mataimakin gwamnan a kan mukaminsa ba tare da bata lokaci ba.

Haka kuma kotun ta bada umarnin a mayar masa da dukanin wasu hakkokinsa na mataimakin Gwamna.

Shi dai mataimakin gwamnan Alhaji Garba Gadi, majalisar dokokin jihar ce ta tsige shi daga mukaminsa, inda shi kuma ya kai maganar kotu.