Garin dan Dukku: Ba maza sai mata

karancin abinci a Nijar
Image caption Matsalar abinci ta sa maza na yin kaura suna barin matan su

Matsalar karancin abincin da al'umar kasar Nijar ke fuskanta ce ummul'aba'isun ficewar mazaje daga garuruwan su da zummar ketarawa kasashe makwabta dan samun abunda za'a aikewa iyalai.

A garin Dan Duku dake karamar hukumar Mirriyah ta jahar Damagaram inda wakiliyar BBC Tchima Ila Issoufou ta ziyarta, ta taras ba maza sam a garin sai mata.

Kuma matan sun shaida mata cewa suma wannan lamari na damunsu. Ko da yake a cewar matan da gwamnatin kasar ta sama masu ruwa da mazajen garin sun dage kan noman rani.

Mata a wannan gari sun ta shi ne tsaye suna sana'a domin daukar nauyin iyalan su.

Kuma duk da cewa damuna ta tsaya mazan sun fice sun bar kasar abinda yasa matan ke fafutukar neman na kalaci.

Malam Murjanatu wacce na daya daga cikin matan garin ta shaidawa BBC cewa babbar matsalar da suke fama da ita itace ta abinci.

"Wasu ma basa iya aikowa da komai"

Image caption Kungiyoyin agaji da dama sun yi shelar kaiwa kasar agajin kayan abinci

Domin acewarta su mata ba sa noma, kuma wurin noman ba ba shi da yawa, don haka koda suna son yi ba za su samu dama ba.

"Abinda mazan suka tafi suka barmana da rani shi muke ci, kari kan abinda suka aikomana, wasu ma basa iya aikowa da komai domin ai sai mun samu sana'ar yi tukunna sannan za su iya aiko da wani abu," in ji Murjanatu.

To ko ta yaya matan ke samun damar daukar dawainiyar yaran da mazan suka tafi suka bar musu, Shamsiyya cewa ta yi:

"Idan aka sare itace na makiyaya sai mudauko mu shanya shi domin ya bushe, daga nan kuma mu sayar domin sayen abincin da za mu bai yara".

Takara da cewa wasu matan kuma kira suke yi da gini domin samun kalace, sai dai zuwan damuna ta sa ruwa ya cinye ma'aikatar ta su.

Rashin ruwa

Wasu da dama na alakanta matsalar da rashin ruwa, wanda kuma yakan hanasu damar yin noman rani, kuma Malama Hadiza ta shaidawa wakiliyar BBC Tchima Ila Issoufou.

Tace: "Da muna da rijiyoyi irin na birni da mun yi noman rani, kuma da maganar a tafi wata kasa neman kudi bata ma ta soba".

Ta kara da cewa baya ga matsalar ruwan noman rani, ruwan sha ma bai ishe su ba, domin sai sun yi tafiya mai nisa sannan suke samun ruwan, kuma baya daukuwa sai a Amalanke.

Matan dai sun nuna rashin jin dadin su, inda suka nemi hukumonin garin da su samar musu da ruwan sha, domin a cewar su wannan itace matsar da ke ci musu tuwo a kwarya.