Yara goma sha biyu sun mutu saboda yunwa a Sakkwato

Nijeriya
Image caption Nijeriya

Hukumomin lafiya a jihar Sakkwaton Nijeriya sun tabbatar da mutuwar yara goma sha biyu a yankin karamar hukumar Gada mai Makwabtaka da jamhuriyar Nijar Sakamakon matsalar yunwa.

Yaran dai na daga cikin yara dubu daya da dari uku da ake kulawa da su a wata cibiya da aka kafa kimanin watanni ukun da suka wuce a yankin bayan gano alamun rashin isasshen abinci a jikinsu.

Wannan matsala ta yunwa dai tasa asusun lura da kananan yara na majalisar dinkin duniya ya yi kira ga kasashen duniya da su tallafawa jamhuriyar kan wannan matsala.

Bayan wannan sanarwa kuma sai gashi jami'ai a jihar Sakkwato mai makwabtaka da Nijar sun tabbatar da wannan lamari.