'Yan siyasar Amurka sun amince da gagrumin gyara ga bankuna

Ginin majalisar dokokin Amurka
Image caption Ginin majalisar dokokin Amurka

'Yan siyasa a Amurka sun amince da gagarumin garan-bawul ga dokokin bankuna bayan sunkwashe tsawon daren jiya suna muhawara.

Manufar kudurin dokar shi ne takaita karfin manyan bankuna ta yadda ba zasu iya shiga mu'amalolin dake da hadari da haddasa matsin tattalin arziki na duniya.

Shugaba Obama yayi marhabin da ci gaban da aka samu, yana mai cewar sauye sauyen za su sa jama'ar Amurka su riki cibiyoyin hada hadar kudi da alhaki.

Ana sa ran dukanin majalisun za su amince da tsarin dokar a cikin mako mai zuwa sannan Shugaban kasa ya sa hannu a kanta.