Mr. Geithner ya kalubalanci kassahen turai

Sakataren baitulmalin Amurka Timothy Geithner
Image caption Sakataren baitun malin kasar amurka ya kalubalanci shugabanni a nahiyar turai da su cigaba da rage kashe kudaden gwamnati

Sakataren baitul malin kasar Amurka Timothy Geithner ya kalubalanci shugabanni a nahiyar turai dasu maida hankali wajen ci gaba da zabtare yawan kudaden da kasashen ke kashewa.

A wata hira da BBC gabannin fara taron kasashen G8 a Canada, Mr Geithner ya ce tilas ne a maida hankali wajen samun ci gaba.

Koda yake Mr. Geithner ya ce mai yiwuwa Amurka da sauran kasashen turai su dauki matakai daban daban wajen magance matsalar koma bayan tattalin arziki.

Mr Gaithener ya ce nahiyar turai nada zabi kan ta samar da sauye sauye ko tsare tsaren da zasu bada damar karfafa matakan samun ci gaba a nan gaba