An kasa cimma matsaya akan lu'u lu'un Zimbabwe

Shugaba Robert Mugabe na kasar Zimbabwe
Image caption Kungiyar Kimberly Process taki amincewa akan zimbabwe ta cigaba da fitar da ma'adinin lu'u lu'u

Kungiyar dake kula da cinikin ma'adinan lu'u'lu'u da ake cewa Kimberly Process taki amincewa da cewa ko zata bar kasar Zimbabwe ta ci gaba da sayar da ma'adinan ta na lu'u'lu'u.

Ana saran dai za'a ci gaba da tattaunawa ne akan wannan batu a wata mai zuwa.

Ita dai kunigyar tana gudanar da harkokin ta ne ta hanyar yarjejeniya, kuma bayan data kammala tattaunawa a kasar Israila, ta ce an kasa cimma matsaya ne kan wannan batu, sakamakon tsare wani mai fufutikar kare hakkin bil'adama daya dade yana sukar yadda ake gudanar da aikace aikace a wurin hakar ma'adinan lu'u'lu'u dake kasar.

Kimberly Process ta dakatar da fitar da ma'adinin daga kasar a watan Nuwambar shekarar bara

Masu fafutuka 'yan adawa dai a Zimbabwen sun zargi manyan jami'an gwamantin kasar da azurta kansu ta hanyar fitar da lu'u lu'un.

Ita kuwa gwamnatin Zimbabwen cewa tayi kasashen yamma ne keyi mata kafar ungulu don gudun kada kasar ta samu cigaban tattalin arziki