Shugaba Obama ya gayyaci wasu shugabannin Afirka

Shugaba Obama na Amurka
Image caption Shugaba Obama na Amurka ya gayyaci wasu shugabannin kasashen afirka goma sha takwas zuwa washington domin bukukuwan tunawa da 'yancin kan kasashen

Shugaban Amurka Barack Obama wanda mahaifinsa dan asalin kasar Kenya ne ya gayyaci wasu shugabannin kasashen Afrika goma sha takwas zuwa Washignton a watan Agusta don bukin cika shekaru hamsin na samun 'yancin kan kasashen su.

Shi dai mahaifin shugaba Obama yayi karatun sa ne a Amurka inda daga bisani ya koma aiki bayan samun 'yancin kai a kasar Kenya

Sai dai an bayyana cewa ya rasu yana cike da nadamar abubuwan da suka faru bayan da aka kawo karshen mulkin turawan mulkin mallaka a wancan lokacin.