Burtaniya da Rasha zasu daidata tsakaninsu

Firayim Ministan Burtaniya David Cameron
Image caption Kasashen Burtaniya da Rasha sunce zasu sake kulla dangantakar dake tsakaninsu

Kasashen Burtaniya da Rasha sun ce zasu sake kulla dangartakar dake tsakanin su bayan da suka kwashe shekaru suna takun saka.

Da yake magana bayan ganarwarsa ta farko ido da ido da Prime Ministan Burtaniya a taron kasashen G8, shugaban kasar Rasha, Dmitry Medvedev ya ce sun dukufa wajen ganin sun sake karfafaka dangartakar dake tsakanin su.

Ana sa bangaren Prime Ministan Burtaniya David Cameron ya ce an samu yanayi da zai kawo sauyi a al'amura.

A kwanakin baya ma dai, kasar Amurka da Rashan sunce zasu inganta dangantakar dake tsakaninsu