Tarayyar Afirka ta damu dangane da zaben Burundi

Al'ummar kasar Burundi
Image caption Shugaban kungiyar tarayyar Afirka ya bayyana damuwarsa dangane da zaben kasar Burundi

Shugaban kungiyar tarayyar Afrika Jean Ping, ya ce yana cike da damuwa dangane da zaben shugaban kasar Burundi da za'a gudanar a ranar litini din nan mai zuwa.

Shugaban kasar mai ci yanzu Pierre Nkurunziza, shine dan takara daya tal da zai tsaya zaben bayan da sauran 'yan takara na jam'iyun adawa suka ki shiga zabe sakamakon zargin tafka magudi a wasu zabubbuka da aka gudanar a kasar.

A wata sanarwa shugaban kungiyar, ya yi kira ga 'yan jam'iyun adawa a kasar da su yi amfani da matakan shari'a kadai wajen warware dukkan takaddamar dake tsakanin su.

Shi dai Jean Ping, ba kasafai yake nuna damuwarsa kan zabubbuka a kasashen Afrika ba, a don haka ganin yanda ya fito ya roki 'yan siyasar kasar, alama ce dake nuna cewa al'amarin nada matukar damuwa.