Taron shugabannin kasashen G8 a Canada

Taron kungiyar kasashen G8 a canada
Image caption Taron kungiyar kasashen G8 a canada ya jaddada bukatar cika irin alkawuran da shugabannin kasashen suka dauka

Shugabannin kasashen duniya masu ci gaban masana'antu na gudanar da wani taro a Canada a karkashin kungiyar kasashe na G8 da G20, inda sauye sauye a bangaren bankuna da matsalar koma bayan tattalin arziki suka kasance muhimman batutuwa a zauren taron.

Firayim Ministan Canada Stephen Harper ya jaddada cewa kamata yayi kasashen G8 su cika alkawuran da suka dauka na taimakawa kasashen Afrika.

Har wa yau a taron kasashen na G8, kasashen Amruka da Burtaniya sun bukaci sauran kasashe da su cika alkawuran bada tallafin da suka dauka a shekarar 2005.