Taron kungiyar Kasashen G8 a canada

Taron kungiyar kasashen G8 a canada
Image caption Taron kungiyar kasashen G8 a canada sun bukaci kasashen dake cikin kungiyar da su cika alkawuran da suka dauka

Shugabannin kasashen duniya masu ci gaban masana'antu na gudanar da wani taro a Canada a karkashin kungiyar kasashe na G8 da G20, inda sauye sauye a bangaren bankuna da matsalar koma bayan tattalin arziki sukai kane kane a zauren taron.

Firayim Ministan Canada Stephen Harper ya jaddada cewa kamata yayi kasashen G8 su cika alkawuran da suka dauka na taimakawa kasashen Afrika.

Har wa yau a taron kasashen na G8, kasashen Amurka da Burtaniya sun bukaci sauran kasashe da su cika alkawuran bada tallafin da suka dauka a shekarar 2005.

Amurka da Burtaniya da Canada dai sun cika alkawarin da suka dauka, sai dai kasashen Faransa da Jamus sun gaza wajen cika nasu alkawuran, yayin da kasar Italiya kuwa ta gaza cika koda abu guda daga cikin alkawuran data dauka.