Ban Ki- Moon ya nemi kasashe masu arziki su cika alkawari

Babban sakataren majalisar dinkin duniya Ban Ki-Moon
Image caption Babban sakataren majalisar dinkin duniya Ban Ki-Moon ya bukaci kasashe masu arziki da su cika alkawarin da sukayi

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki- Moon ya yi kira ga kasashe masu arziki dasu cika alkawuran da suka dauka na bada tallafin dala biliyan hamsin a shekarar 2005.

A wata hira da BBC bayan da kasashen G8 suka kammala ganawa a Canada, gabannin fara taron kasashen G20, Mr Ban Ki- Moon yayi gargadin cewa matsalar koma bayan tattalin arziki na matukar barazana ga cimma burin muradun karni na Majalisar Dinkin Duniya a shekarar 2015.

Ya ce muddin fa kasashen da suka ci gaba, suka cika alkawuran da suka dauka kuma muddin kasashen masu tasowa zasu inganta matakan gwamnatoci tare da magance matsalar cin hanci da rashawa, to kuwa hakika za'a iya cimma burin muraddun karnin a shekarar 2015.